Yadda masu kuɗi ke lalata ƴaƴan talakawa a Kano – Daurawa
Shugaban Hukumar Hizba ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana takaici kan yadda tarbiyya ke ƙara taɓarɓarewa tsakanin al’umma a jihar.
Malamin ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC.
Kano da ke arewacin Najeriya jiha ce mai yawan al’umma kuma cibiyar kasuwanci a yankin.
Duk da cewa akwai ƙabilu da yawa da suke zaune a jihar amma kasarin al’ummarta mabiya addinin musulunci ne.
Wannan ya sanya koyarwa da al’adu na addinin musulunci ke da matuƙar tasiri, lamarin da ya sanya gwamnatin jihar ta kafa hukumar Hisba wadda aka ɗora wa alhakin tabbatar da cewa al’umma na bin dokoki addinin na Musulunci.
Sai dai a kwankin baya-bayan nan ayyukan hukumar ya riƙa haifar da cecekuce da muhawarori.
Na baya-bayan nan shi ne yanda hukumar ke takun-saƙa tsakanin ta da masu wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta, musamman tiktok.
Sai dai ba wannan ne kaɗai matsalar ba, Sheikh Aminu Daurawa ya ce abubuwan na rashin tarbiyya da ake aikatawa a jihar na ƙara muni, kuma za su ci gaba da munana matuƙar ba a ɗauki matakan da suka dace ba.
Ɗaya daga cikin abubuwan da ya ce a yanzu hukumar na fama da su shi ne batun lalata ƙananan yara.
A cewarsa “Yanzu akwai wasu yara ƴan shekara 13, mun samu guda biyu suna ɗauke da ciki.”
Ya bayyana cewa irin waɗannan yara su ne waɗanda iyayensu ke ɗora wa talla, amma ake kai su otal-otal domin yin lalata.
Ya ƙara da cewa mutanen da suke aikata abubuwan da ba su dace da yaran “sun hana yara yin karatu kuma suna hana su yin sana’a.”
Ko a kwanakin baya jami’an hukumar ta Hisba sun kai samame a wasu otal-otal da ke birnin Kano domin kama mutanen da ake zargi da aikata ayyukan da suka saɓa wa dokokin addinin Musulunci.
Sai dai bidiyon irin waɗannan samame da jami’an hukumar suka kai sun haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta.
Inda wasu al’ummar ke ganin cewa matakin tamkar take hakkin al’umma ne na ƴancin walwala.
Yayin da kuma wasu ke ganin rashin dacewar yadda jami’an hukumar suka riƙa ingiza mata cikin motoci.
Sai da a tattaunawar tasa da BBC, Sheikh Daurawa ya ce akan tursasa wa waɗanda suka turje ne kawai.
Ya bayyana cewa a lokutan irin waɗannan samame akan buƙaci wadanda ake zargi su shiga mota cikin lalama, sai dai wasu daga ciki kan ƙi bin umarnin jami’an.
'Muna sa ido kan shafukan ƴan tiktok 70'
Daurawa ya bayyana cewa bayan hukumar ta gayyaci masu sanya bidiyo a shafukan tiktok tare da yi musu nasiha yanzu haka an zakulo shafuka 70 waɗanda ake sanya ido a kansu.
A cewarsa tuni hukumar ta tuntuɓi kamfanin tiktok, wanda ya yi alƙawarin toshe shafin duk wani ɗan tiktok da ya saɓa doka.
A baya, shugaban na Hisba ya gayyaci wasu da suka shahara a shafukan na tiktok inda ya tattauna da su.
Kamar yadda hukumar ta bayyana, ta gayyace su ne domin yi musu nasiha kan abubuwan da ta bayyana a matsayin waɗanda suka saɓa wa dokar Musulunci da al’adun al’ummar jihar.
‘Siyasa na yi wa ayyukan Hisba tarnaƙi’
Malam Aminu Daurawa ya ce siyasa na daga cikin manyan ƙalubalen da hukumar Hisba ke fuskanta.
A cewarsa: “Wani da za ka taba ɗan wata jam’iyya ne”, ya ƙara da cewa irin waɗannan mutane sukan fusata a duk lokacin da hukunci ya hau kansu saboda “suna ganin ba a kyauta musu ba.”
Ya ce “Akwai waɗanda suke jin cewa sun fi ƙarfin doka” ya ƙara da cewa “suna ganin babu wanda ya isa ya yi musu nasiha ko ya hukunta su saboda sun fi ƙarfin kowa, muna da irin su da yawa.”
“Akwai wani mai sarauta da aka kama yana lalata yara, ya kira ni yana ta zage-zage.”
Gyare-gyaren da ake yi wa Hisba
A cewar Malam Aminu Daurawa a yanzu hukumar Hisba ta tsagaita kan yadda take gudanar da ayyuka a baya domin gudanar da wasu sauye-sauye.
Cikin abubuwan da Hukumar ke shirin aiwatarwa akwai ƙara bai wa jami’anta horo, da neman ƙarin kuɗaɗen tafiyar da ayyuka saboda tsadar man fetur na zirga-zirga.
Haka nan ya ce hukumar na shirin gayyato masu gidajen otal-otal domin tattaunawa da su.
Ya ce za a gayyaci masu otal-otal ɗin ne domin fadakar da su kan ayyukan hukumar da kuma neman su sanya hannu kan yarjejeniyar kiyaye ƙa’idoji.
Comments