Gwamnan Gombe ya jinjina wa yarinyar da ta lashe gasar karatun Al-Ƙur'ani ta duniya
Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana farin cikinsa game da nasarar da Hajara Ibrahim Dan'azumi - wata matashiya ƴar jihar ta samu ta lashe gasar karatun Al-Qur'ani ta duniya da aka yi a ƙasar Jordan.
An zaɓi Hajara Ibrahim daga makarantar Islamiyya ta Abubakar Siddiq wadda ɗaliba ce ƴar aji biyu da ke karatun ilimin tsirrai daga jami'ar jihar Gombe ta wakilci Najeriya, inda kuma ta lashe gasar cikin mutane daga ƙasa 39 da suka halarci gasar karo na 18 da ma'aikatar kula da harkokin musulunci da ba da zakka da hubusi ta Jordan ke shiryawa duk shekara.
Da yake tsokaci kan batun, Gwamna Inuwa Yahata ya miƙa saƙon taya murna ga Hajara da danginta da kuma malamanta inda ya yaba da ƙoƙarinta da jajircewarta wajen haddace Al-Qur'ani.
Ya kuma bayyana cewa nasarar da ta samu zai zama ƙwarin gwiwa ga mutane da dama da ke Gombe da wasu jihohin.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin kula da kuma tallafawa matasa ta ɓangaren karatunsu musamman na addini abin da ya ce yana taka rawa sosai wajen gyara halayyarsu da kuma ba da gudummawa ga ci gaban al'umma
Comments