A wani gagarumin ci gaba na fadada sawun sa, bankin Alternative ya yi alfahari da bude reshensa na farko a cikin birnin Kano mai tarihi, inda ya samu amincewar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a hukumance. Sarkin, a cikin jawabinsa ya yaba wa bankin Alternative a matsayin wani yunkuri na kawo sauyi da ke shirin yin tasiri sosai ga mutane da ‘yan kasuwa a jihar. Ya jaddada muhimmiyar rawar da cibiyoyin hada-hadar kudi ke takawa wajen tsara al’amuran al’umma ta wannan zamani. Ya amince da kudurin Bankin Madadin ga ayyukan da'a, nuna gaskiya, da inganta ci gaban tattalin arziki mai dorewa a yankin. Shima da yake jawabi a wajen kaddamar da reshen, Babban Daraktan Bankin Alternative, Garba Mohammed, ya bayyana bankin a matsayin mai da’a. Mohammed ya ce, “Muna alfahari da kasancewa cikin wannan gagarumin biki domin kaddamar da fara wannan bankin, wanda ko shakka babu zai yi matukar amfani ga al’ummarmu.