FBI ta bayyana sunan mutumin da ya yi yunƙurin kashe Trump
FBI ta bayyana sunan mutumin da ya yi yunƙurin kashe Trump ASALIN HOTO Hukumar tsaro ta FBI ta bayyana sunan mutumin da ake zargi da yunƙurin kashe tsohon shugaban Amurka Donald Trump a wajen yaƙin neman zaɓe. Hukumar ta ce sunan mutumin Thomas Matthew Crooks, kuma ɗan asalin yankin Bethel park ne a Pennysylvania. FBI ta ce tana binciken lamarin a matsayin yunƙurin kisan kai, kuma ba zata yi ƙasa a gwiwa ba wajen kammala bincike. Hukumar ƴan sandan Pennsylvania ta ce hankali ya kwanta a yankin domin kuwa babu sauran barazanar aikata wani laifin mai kama da wannan. Hukumar leƙen asirin Amurka ta ce ''an harbe mutanen da ake zargi da kai harin kuma ya mutu nan take,'' kamar yadda mai magana da yawun hukumar Anthony Guglielmi ya tabbatar. Ya ƙara da cewa akwai wani ɗan kallo da aka kashe a wajen, yayin da wasu mutane biyu suka samu rauni. FBI ta ce mutumin da ake zargin ba ya ɗauke da wata shaida mai bayani a kansa, amma za a gudanar da gwajin ƙwayar halitta domin gano c...