Posts

Showing posts from March, 2024

Kano Ta Tallafawa Alhazai 2,096 Da Naira Biliyan 1.4

Image
 Kanawa post news  Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da bayar da tallafin Naira 500,000 ga kowane mahajjaci daga jihar. Tallafin ya biyo bayan umarnin da Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta bayar, inda ta bukaci maniyyatan da su biya karin Naira miliyan 1.9 na kudin Hajjin shekarar 2024. Dole Ne Mu Ajiye Bambancin Addini, Ƙabilanci Da Siyasa A Baya – Ministan Yaɗa Labarai Gwamnatin Nijeriya Ta Bayar Da Tirela 100 Na Shinkafa, Dawa Da Masara A Raba A Kano Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Dan Baffa ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai ranar Laraba a Kano. A cewarsa, gwamnatin jihar za ta biya jimillar kudi naira biliyan 1.4 ga maniyyata 2,096 da suka yi niyyar aikin hajjin bana. Ya ce, gwamnatin jihar Kano ta dauki wannan matakin ne duba da karin kudin aikin Hajji da hukumar alhazai ta kasa ta yi a baya-bayan nan wanda a cewarta, karin an yi shi ne biyo bayan faduwar darajar Naira kan canjin Dalar Amurka.

Ɗantakarar shugaban Senegal na jam'iyya mai mulki ya taya na adawa murna

Image
  Bassirou Diomaye Faye Yayin da al'ummar ƙasar Senegal ke jiran hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar Lahadi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki Amadou Ba ya taya ɗan takara na haɗakar ƴan adawa Bassirou Diomaye Faye murnar samun nasara. Alƙaluman da jam'iyyun siyasar ƙasar ke tattarawa bayan rufe rumfunan zaɓe a jiya Lahadi sun nuna cewa Bassirou Faye na jam'iyyar adawa shi ne ke kan gaba a yawan ƙuri'un da za su iya ba shi nasara kai-tsaye. Har yanzu dai babu wani sakamako da ya fito daga hukumar zaɓen ƙasar, wadda ke ci gaba da tattara sakamakon, kuma ba za ta bayyana ƙuri'un da kowane ɗantakara ya samu ba sai ta kammala haɗa alƙaluma. Taya Faye murna da Amadou ya yi ya zo wa al'umma da mamaki, ganin irin hamayya mai ƙarfi da ke tsakanin ɓangarorin biyu. A cikin sanarwar da ya fitar, Amadou Ba ya ce: "Ganin irin bayanan da ke fitowa game da zaɓen shugaban ƙasa, yayin da muke ci gaba da jiran ...

Dalilin da ya sa hukumar Alhazan Najeriya ta ƙara kusan naira miliyan biyu

Image
Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajji da miliyan ɗaya da dubu ɗari tara, inda yanzu kuɗin suka koma naira miliyan shida da dubu 800 kan kujera ɗaya. Hukumar ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin dala wadda da ita ce ake yin kiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke bukata. Mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta ce wadanda ba su fara biyan wani abu daga cikin kudin kujerar ba za su biya naira miliyan takwas, saboda lokacin da aka fitar da farashin kujerar aikin Hajjin bana dala ba ta yi tashin da ta yi ba yanzu. Hukumar ta kuma ba maniyyata aikin Hajjin na bana wa'adin zuwa 29 ga watan nan na Maris da ake ciki domin kammala biyan kudin: " Wadanda suka kasa biya suna da zaɓi biyu ko dai su rubuta a mayar masu da kuɗinsu ko kuma su ajiye kudin har zuwa shekara mai zuwa." Hukumar ta ce mutum 49,000 ne suka biya kudin kujerun a farashin baya daga cikin kujeru 75,000 da Saudiya ta ba mahajjan gwamnati yayin da ƴan kas...