Posts

Showing posts from July, 2024

FBI ta bayyana sunan mutumin da ya yi yunƙurin kashe Trump

Image
  FBI ta bayyana sunan mutumin da ya yi yunƙurin kashe Trump ASALIN HOTO Hukumar tsaro ta FBI ta bayyana sunan mutumin da ake zargi da yunƙurin kashe tsohon shugaban Amurka Donald Trump a wajen yaƙin neman zaɓe. Hukumar ta ce sunan mutumin Thomas Matthew Crooks, kuma ɗan asalin yankin Bethel park ne a Pennysylvania. FBI ta ce tana binciken lamarin a matsayin yunƙurin kisan kai, kuma ba zata yi ƙasa a gwiwa ba wajen kammala bincike. Hukumar ƴan sandan Pennsylvania ta ce hankali ya kwanta a yankin domin kuwa babu sauran barazanar aikata wani laifin mai kama da wannan. Hukumar leƙen asirin Amurka ta ce ''an harbe mutanen da ake zargi da kai harin kuma ya mutu nan take,'' kamar yadda mai magana da yawun hukumar Anthony Guglielmi ya tabbatar. Ya ƙara da cewa akwai wani ɗan kallo da aka kashe a wajen, yayin da wasu mutane biyu suka samu rauni. FBI ta ce mutumin da ake zargin ba ya ɗauke da wata shaida mai bayani a kansa, amma za a gudanar da gwajin ƙwayar halitta domin gano c...

Shugabannin duniya sun bayyana alhini kan harin da aka kai wa Trump

Image
  Shugabannin duniya sun bayyana alhini kan harin da aka kai wa Trump Shugabannin duniya sun bayyana alhini kan harin da aka kai wa Trump ASALIN HOTON, AP Shugabannin ƙasashen duniya sun mayar da martani da kaɗuwa dangane da harin da aka kai wa Donald Trump. Firaiministan Burtaniya, Keir Starmer, ya ce ya yi matukar kaɗuwa da labarin harin. Takwaransa na Hungary Viktor Orban wanda ya ziyarci Mista Trump kwanan nan, ya ce yana sanya shi a addu'a, yayin da Narendra Modi na Indiya ya ce tashin hankali ba shi da gurbi a tsarin dimokuradiyya. Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce ya yi mamakin faruwar lamarin, to amma yana masa fatan samun lafiya. Shugaban Argentina, Javier Milei, ya nuna fushinsa, inda ya zargi masu sasaucin ra'ayi da rungumar ta'addanci, maimakon tafarkin dimukradiyya